IQNA

An Fara Gudanar Zaman Taron Al'adun Muslunci A kasar Amurka

16:36 - January 20, 2011
Lambar Labari: 2067896
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da zaman taron muslunci da kuma al'adunsa acikin kasar Amurka, da ke samun halartar mabiya addinin muslunci da kuma masana da aka gayyata daga sassa na kasar, wanda yanzu haka taron na gudana abirnin Chicago.


Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam today cewa, an fara gudanar da zaman taron muslunci da kuma al'adunsa acikin kasar Amurka, da ke samun halartar mabiya addinin muslunci da kuma masana da aka gayyata daga sassa na kasar, wanda yanzu haka taron na gudana abirnin Chicago na kasar ta Amurka.

Bayanin ya ci gaba da cewa musulmin kasar Amurka suna gudanar da taruka lokuta da dama da nufin wayar da kan al'ummar kasar da suke da mummunar fahimta kan addinin muslunci, sakamakn jahilcinsu da shi da koyarwarsa, da kuma siyasar da aka dora su a kanta ta nuna kyama ga wannan addini mai tsarki.

Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da zaman taron muslunci da kuma al'adunsa acikin kasar Amurka, da ke samun halartar mabiya addinin muslunci da kuma masana da aka gayyata daga sassa na kasar, wanda yanzu haka taron na gudana abirnin na Chicago.

733336


captcha