Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an habarta cewa, ministocin harkokin cikin gida na kasashne musulmi za su gudanar da zama domin yin bahasi kan yanayin da kananan yara suke ciki a kasashen musulmi, wanda za a gudanar a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya, wanda cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adun musulunci ta duniya za ta dauki nauyin shirayawa da gudanarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zama zai yi dubi ne matsaloli da kanan yara suke fuskanta a wasu kasashen musulmi, wanda ya zama wajibi a gabatar musu da dukkanin taimakon da suke bukata domin warware matsalolinsu gwargwadon iko, da kuma yadda musulmi za su iya taka rawa kan hakan.
Ministocin harkokin cikin gida na kasashne musulmi za su gudanar da zama domin yin bahasi kan yanayin da kananan yara suke ciki a kasashen musulmi, wanda za a gudanar a birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libya, wadda daya ce daga kasashe mambobi a cibiyar.
734520