Bangaren kasa da kasa, Za a bude wani babban shafin sadarwa na yanar gizo na addinin muslunci a kasar Saudiyya, wanda ma'aikatar kula da ayyukan Musulunci ta kasar za ta dauki nauyin ayyukansa, wanda zai fara aiki daga yau.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama na kasar Malazia an bayyana cewa, za a bude wani babban shafin sadarwa na yanar gizo na addinin muslunci a kasar Saudiyya, wanda ma'aikatar kula da ayyukan Musulunci ta kasar za ta dauki nauyin ayyukansa, wanda zai fara aiki daga yau Lahadi.
Ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci na kasar Saudiyya ya bayyana cewa, babbar manufar samar da wannan shafi ita ce yada manufofin addinin Musulunci da koyarwarsa a sassa daban-daban na duniya ta hanya mafi sauki, wato hanyar sadarwa ta yanar gizo, wadda mutane suke amfani da ita ko'ina a fadin duniya.
Bude babban shafin sadarwa na yanar gizo na addinin muslunci a kasar Saudiyya, wanda ma'aikatar kula da ayyukan Musulunci ta kasar za ta dauki nauyin ayyukansa, wanda zai fara aiki daga yau, na da matukar muhimmanci wajen isar da sako a cikin yarukan da za a yi amfani da su a cikinsa.
735090