IQNA

18:16 - January 26, 2011
Lambar Labari: 2070863

An Fara Gudanar Da Zaman Taro Na Kasa Da Kasa Na Abincin Halal A Kuwait

Bangaren kasa da kasa, An fara gudanae da wani zaman taro kan abincin halal a mataki na kasa da kasa wanda ya hada dukkanin kasashen tekun fasha a kasar Kuwait, tare da halartar wakilai daga kasashe daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA an bayyana cewa, an fara gudanae da wani zaman taro kan abincin halal a mataki na kasa da kasa wanda ya hada dukkanin kasashen tekun fasha a kasar Kuwait, tare da halartar wakilai daga kasashe daban-daban na larabawan tekun fasha.
Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait ita ce ta dauki nauyin shirya wannan zaman taro, wanda kuma ya fao ne daga wani shiri da kasar Malazia ta kirkiro na fayyace abincin halal ga mabiya addinin musulunci a duk inda suke duniya, ta yadda za su samu saukin gudanar da lamurransu ba tare da fuskantar matsa ta fuskacin abinci da yake halal a addininsu ba.
An fara gudanae da wani zaman ne taro kan abincin halal a mataki na kasa da kasa wanda ya hada dukkanin kasashen tekun fasha a kasar Kuwait, tare da halartar wakilai daga kasashe daban-daban, da nufin karfafa harkar samar da abincin halal a yankin.

736329




captcha