Bangaren kasa da kasa, An gudanr da wani zaman taro mai taken fahimtar kur'ani mai tsarki a jahar Georgia ta kasar Amurka, da nufin fadada bincike kan ma'nonin kur'ani da kuma aikata umurininsa a cikin rayuwa ta zamantakewa da ta kebanci musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aluka.net an bayyana cewa, an gudanr da wani zaman taro mai taken fahimtar kur'ani mai tsarki a jahar Georgia ta kasar Amurka, da nufin fadada bincike kan ma'nonin kur'ani da kuma aikata umurininsa a cikin rayuwa ta zamantakewa da ta kebanci musulmi a duk inda suke a fadin duniya.
Wannanzaman taro dai ya samu halartar masana da malaman addinin Musulunci daga sassa dabandaban na kasar Amurka, kamar yadda ya samu halartar wasu wadanda ba mabiya addinin Musulunci ba ne, domin samun karin haske kan koyarwar addini.
An gudanr da wani zaman taro mai taken fahimtar kur'ani mai tsarki a jahar Georgia ta kasar Amurka, da nufin fadada bincike kan ma'nonin kur'ani da kuma aikata umurininsa a cikin rayuwa ta zamantakewa da ta kebanci musulmin kasar.
737536