Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Montana.edu an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro mai taken makomar dangantaka tsakanin addinin muslunci da kuma al'ummomin kasashen yammacin duniya, wanda za a gudanar a jami'ar monatana ta kasar Amurka tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka masana musulmi daga birnin New York cibiyar kasuwancin kasar Amurka na da shirin halartar wannan zaman taro, inda za su gabatar da makalolin da suka rubuta kan maulun taron, haka nan kuma za a gabatar da laccoci kan hakan.
Manufar gudanar da wannan zaman taro dai ita ce fadakar da mahukunta da kuma masana da wadanda suke da 'yancin tunani a cikin kasashen yammacin turai, da su dawo daga rakiyar tunanin gaba da addinin Musulunci, domin kuwa shi addini ne na rahma.
Gudanar da zaman taro mai taken makomar dangantaka tsakanin addinin muslunci da kuma al'ummomin kasashen yammacin duniya, wanda za a gudanar a jami'ar monatana ta kasar Amurka tare da halartar masana, na da muhimmanci wajen fito da mahangar Musulunci.
740257