IQNA

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Nigeria

16:25 - February 03, 2011
Lambar Labari: 2074682
Bangaren kasa da kasa, Ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a karo na ashirin da biyar a jahar Bauchi, wadda aka fara gudanarwa tun a ranar Lahadi da ta gabata tare da halartar makaranta daga sassa na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jahar Bauchi punchng an bayyan acewa, ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a karo na ashirin da biyar a jahar Bauchi, wadda aka fara gudanarwa tun a ranar Lahadi da ta gabata tare da halartar makaranta daga sassa na kasar, musamman ma daga jahohin arewa.
Bayanin ya ci gaba da cewa ana gudanar da gasar ne a bangarori shida, da suka hada da bangaren karatu zalla, sai kuma bangaren ilimin sanin ka’idojin karatun kur’ani mai tsarki wato tajwidi, haka nan kuma na kasa bangarorin karatun kashi-kashi, bisa la’akari da matsayin hardar mahalarta gasar.
Rahoton ya ce yanzu haka a halin da ake ciki ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a karo na ashirin da biyar a jahar Bauchi, wadda aka fara gudanarwa tun a ranar Lahadi da ta gabata tare da halartar makaranta daga cikin jahar da kuma sauran jahohi.
740631


captcha