Bangaren kasa da kasa, An bude wani baje koli na kayayyakin fasaha a garin Aljarudiyya da ke cikin lardin Katif a gabacin kasar Saudiya, wanda aka yi wa take da yunkurin Imam Hussain (AS) wanda yake gudana a Husainiyar Imam Zainul abiding (AS) da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkauthar an bayyana cewa, a bude wani baje koli na kayayyakin fasaha a garin Aljarudiyya da ke cikin lardin Katif a gabacin kasar Saudiya, wanda aka yi wa take da yunkurin Imam Hussain (AS) wanda yake gudana a Husainiyar Imam Zainul abiding (AS) da ke birnin na Aljarudiyya.
An bude wannan taron baje koli ne tun ranar Alhamis da ta gabata, inda a ranar farko aka kebance wa mata shiga wurin domin gane wa idanunsu abubuwan da aka baje a wurin, a rana ta biyu kuma aka kebance ma maza ranar domin su shiga wurin.
Daga cikin abubuwan da ake nunawa a wannan baje koli hard a wasu hotuna na zane kan waki'ar ranar Ashura, da kuma wasu daga cikin alluna da aka yi da suke yin nuni da Imam Hussain da kuma sahabbansa da sauran iyalan gidan manzo a ranar.
Haka nan kuma an nuwa wasu rubuce-rubuce na hannu duk da suke hakaita ranar Ashura da kuma, da kuma yanayin da iyalan gidan manzon Allah suka samu kansu a ciki a ranar.
741721