IQNA

Wasu Kanan Hukumomi Ba Su Halarci Gasar Kur'ani A Jahar Bauchi Ba

11:53 - February 08, 2011
Lambar Labari: 2077466
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin jahar Bauchi ta bukaci kanan hukumomin da ba su halarci gasar karatun kur'ani da aka gudanar a jahar ba da su yi karin bayani kan dalilansu na yin hakan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Trust cewa gwamnatin jahar Bauchi ta bukaci kanan hukumomin da ba su halarci gasar karatun kur'ani da aka gudanar a jahar ba da su yi karin bayani kan dalilansu na yin hakan bayan da aka aike musu da goron gayyata a cikin isassen lokaci.

Bayanin ya ci gaba da cewa gwamnan jahar Bauchi ne da kansa ya yi wannan kira a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban mahalarata taron girmama wadanda suka nuna kwazoa a gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a jahar, wadda ta samu halartar wakilai daga jahohi talatin na Nigeria, musamman ma daga jahohon yankunan arewacin kasar.

Wannan dai shi ne karo na ashirin da uku da ake gudanar da wannan gasa a matsayi na kasa baki daya a tarayyar Nigeria, dukkanin wakilan jahohi da suka halarci gasar sun samu kyautuka na musaman da aka bayar, kamar yadda aka bayar da wasu kyautukan ga wadanda suka nuna kwazo musanna matsayi na daya da na biyu da uku.

743358
captcha