IQNA

Bangaren siyasa da zamantakewa;darektoci da shugabannin da kuma ma'aikata na hukumar da ke kula da yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a ciki da wajan kasar bayan sun ziyarci hubbarin Imam Khomeini ® a ranar sha shidda ga watan Bahman shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya sun jaddada mubaya'a ga mu'assasin juyin juya halin .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; darektoci da shugabannin da kuma ma'aikata na hukumar da ke kula da yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a ciki da wajan kasar bayan sun ziyarci hubbarin Imam Khomeini ® a ranar sha shidda ga watan Bahman shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya sun jaddada mubaya'a ga mu'assasin juyin juya halin .A bukin mubaya'a Muhammad Bakir Khuramshad shugaba ma'aikatan hukumar bayan ya mika kyautar hure a lokacin ziyarar da ziyartar wadanda suka yi shahada sun jaddada mubaya'a.


743207