IQNA

Al'ummar Musulmin Malaisiya Na Goyan Bayan al'ummar Masar

13:12 - February 09, 2011
Lambar Labari: 2078390
Bangaren siyasa da zamantakewa: kungiyoyin musulmin Malaisiya bayan sun gudanar da taro a gaban ofishin jakadancin Amerika a a birnin Kwalalampur fadar mulkin kasar sun bayyana goyan bayansu a fili ga gwagwarmayar da al'ummar kasar Masar ke yi.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; kungiyoyin musulmin Malaisiya bayan sun gudanar da taro a gaban ofishin jakadancin Amerika a a birnin Kwalalampur fadar mulkin kasar sun bayyana goyan bayansu a fili ga gwagwarmayar da al'ummar kasar Masar ke yi.A ranara sha biyar ga watan Bahman na wannan sheakara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya wadanda suka halarci wannan zanga-zangar suka nuna goyan bayansu a fili ga al'ummar kasar Masart da suka kaddamar da intfada ta kawo karshen zalunci da danniya da shugaba Husni Mubarraka ya share shekaru talatin yana nunawa al'ummar kasar ta Masar bayan da yake samun goyan Amerika da Haramtacciyar kasar Isra'ila.

743233
captcha