IQNA

Za A Fara Aiwatar Da Wani Shiri Na Horar Yara Da Karatun Kur’ani A Yankin Katif

16:02 - February 09, 2011
Lambar Labari: 2078534
Bnagaren kasa da kasa, Babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki ta yankin Katif a kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta fara aiwatar da wani sabon shiri da ta ke da shi na horar da kananan yara karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki a babbar hedikwatarta da ke garin Zahran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Rasid da ke kasar Saudiyya an bayyana cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki ta yankin Katif a kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta fara aiwatar da wani sabon shiri da ta ke da shi na horar da kananan yara karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki a babbar hedikwatarta da ke garin Zahran.

Shirin zai kebanci yara ne da shekarunsu suka kama daga bakwai zuwa sha biyu, kuma zai dauki kimanin watanni uku ana gudanar da shi, daga cikin muhimman abubuwan da za a koyar har da karatu da kuma sanin ka’idojinsa wato ilimin tajawidi, bayan nan kuma za akoyar da su harda.
Babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki ta yankin Katif a kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta fara aiwatar da wani sabon shiri da ta ke da shi na horar da kananan yara karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki a babbar hedikwatarta da ke garin Zahran.
743673


captcha