Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wam na kasar hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, an kawo karshen zaman taron da ya gudana na ministocin ma'aikatun kula da harkokin kananan yara na kasashen musulmi a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya, wanda ya kwashe tsawon kwanaki ana gudanarwa a birnin.
Rahoton ya ci gaba da cewa baya ga ministocin da suka halarci zaman taron, an samu halartar wasu daga cikin jami'an gwamnatoci na kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, kamar yadda wasu daga cikin mahalarta taron suka bukaci da a gaggauta daukar matakan kawo karshen matsalolin da kananan yara ke fama da su a kasashen musulmi.
A nasu bangaren ministocin da suka halarci zaman taron sun jaddada wajbcin ci gaba da gudanar da irin wannan taro, wanda shi ne irinsa na uku da aka gudanar, saboda amfaninsa ga kasashen musulmi.
746282