Bangaren kasa da kasa, An nuna wasu kwafikwafi na littafan addinin muslunci da aka rubuta kan kur'ani mai tsarki da kyautata rubutunsa daga kasashen musulmi da dama, a tarin rubutun kur'ani na duniya da ake gudanarwa a birnin Madina mai alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran kasar Bahrain an bayyana cewa, An nuna wasu kwafikwafi na littafan addinin muslunci da aka rubuta kan kur'ani mai tsarki da kyautata rubutunsa daga kasashen musulmi da dama, a tarin rubutun kur'ani na duniya da ake gudanarwa a birnin Madina mai alfarma da ke kasar Saudyya.
Wannan taro dai yana samun halaratar marubuta kur'ani mai tsarki daga sassa daban-daban na kasashen musulmi, inda suke nuna fasaharsu da kuma al'ada ta rbutu a Musulunci, daga cikin muhimman abubuwan da taron ya mayar da hanakali kansu har da batun bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka nuna kwazo a taron.
Nuna wasu kwafikwafi na littafan addinin muslunci da aka rubuta kan kur'ani mai tsarki da kyautata rubutunsa daga kasashen musulmi da dama, a tarin rubutun kur'ani na duniya da ake gudanarwa a birnin Madina mai alfarma, na tabbatar da ci gaban da addinin Musulunci ya samu tun tsawon shekaru.
747487