Bangaren kasa da kasa, An buga tare da yada wani littafi na koyon karatun kur'ani mai tsarki da tajwidi a cikin harshen larabci, wanda wanda dalibai masu karatun share fage za su iya amfana da shi a makarantun firamare.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kur'an a n bayyana cewa, an buga tare da yada wani littafi na koyon karatun kur'ani mai tsarki da tajwidi a cikin harshen larabci, wanda wanda dalibai masu karatun share fage za su iya amfana da shi a makarantun firamare da kuma makarantun koyar da kur'ani.
Ya ci gaba da cewa mashahurin marubucin nan kuma malamin kur'ani Haidar ka'abi shi ne ya dauki nauyin rubuta wannan littafi, haka nan kuma ya yi amfani da hanyar koyarwa ta zamani, wadda za ta bai dalibai damar koyon karatun cikin sauki, inda ya kasa littafin zuwa fasali bakwai.
Buga tare da yada wani littafi na koyon karatun kur'ani mai tsarki da tajwidi a cikin harshen larabci, wanda wanda dalibai masu karatun share fage za su iya amfana da shi a makarantun firamar, zai taimaka ma masu koyon karatun kur'ani yara da manya.
749015