Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar mata mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah (SAW) a garin Al'awamiyya da ke cikin lardin Katif, ta shirya gudanar da wani zaman taro na raya ranakun murnr tunawa da zagayowar lokacin maulidin manzon Allah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid ta kasar Saudiyya an bayyana cewa, wata cibiyar mata mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah (SAW) a garin Al'awamiyya da ke cikin lardin Katif, ta shirya gudanar da wani zaman taro na raya ranakun murnr tunawa da zagayowar lokacin maulidin manzon Allah (SAW) a garin.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro da aka fara gudanarwa tun kwanaki biyu da suka gabata, yana yin dubi ne kan abubuwan da suka shafi rayuwar manzo da dabi'unsa, ta yadda dukkanin mutane za su iya yin koyi da rayuwarsa mai albarka a cikin zamantakewarsu.
Cibiyar mata mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah (SAW) a garin Al'awamiyya da ke cikin lardin Katif, ta shirya gudanar da wani zaman taro na raya ranakun murnr tunawa da zagayowar lokacin maulidin manzon Allah.
748980