IQNA

12:43 - February 19, 2011
Lambar Labari: 2083167

Palastinwa Uku Ne Suka Yi Shahada A Wani Harin Ta'addancin Isra'ila A Gaza

Bangaren kasa da kasa, palastinawa uku ne suka yi shahada a yankin Zirin Gaza bayan da sojin yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai wani harin ta'addanci a kan yankunan da fararen hula suke zaune.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar arab on line an bayyana cewa, palastinawa uku ne suka yi shahada a yankin Zirin Gaza bayan da sojin yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai wani harin ta'addanci a kan yankunan da fararen hula suke zaune a yankin.

Sojin yahudawan sun kai harin da manyan kayan yaki da suka hada datankoki da lkuma motocin yaki amsu sulke, inda suka yi ta yin ruwan wuta irin na kan mai uwa da wabi a yankin na bait lahiya, inda suka kashe mutanen uku wadanda dukkanin masu aikin kamun kifi ne.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan harin ta'addanci da sojin yahudawan sahyuniyan suka ya yi kama da irin wanda suka saba kaiwa a kan yankunan palastinawa da suke zaune a yankin zirin gaza, da kuma sauran yankunan gabar yamma da kogin Jordan inda palastinawa 'yan gwagwarmaya suka fi yawa.

A cikin shekara ta 2006 ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da yaki kan al'ummar yankin zirin Gaza, inda ta kwashe tsawon kawanaki sama da ashirin tana kashe kanan yara da mata da kuma fararen hula, amma kuma sun fuskanci turjiya daga masu gwagwarmaya.

Rahoton ya ce palastinawa uku ne suka yi shahada a yankin Zirin Gaza bayan da sojin yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai wani harin ta'addanci a kan yankunan da fararen hula suke zaune.

749815
captcha