IQNA

An Gudanar Da Zaman Taron Darakktocin Cibiyoyin Kur’ani A yankin Zirin Gaza

14:26 - February 20, 2011
Lambar Labari: 2083970
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da zaman babban zaman taro na daraktocin cibiyoin kur’ani mai tsarki da ke yankin Zirin Gaza a masallcin darulkutni da ke gabacin yankin, tare da halartar wasu daga cikin jami’an gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na panet.co.il an bayyana cewa, an gudanar da zaman babban zaman taro na daraktocin cibiyoin kur’ani mai tsarki da ke yankin Zirin Gaza a masallcin darulkutni da ke gabacin yankin, tare da halartar wasu daga cikin jami’an gwamnatin da al’ummar palastinu suka zaba.
Babbar cibiyar darul kur’an da sunna da ke da mazauni a gabacin zirin Gaza ita ce ta dauki nauyin shrya wannan zaman taro, domin yin dubi kan muhimman ayyukan da take gudanarwa da kuma duba ci gaba da matsalolin da aka fuskanta a cikin wannan shekara dangane da ayyukan kur’ani.
An gudanar da zaman babban zaman taro na daraktocin cibiyoin kur’ani mai tsarki da ke yankin Zirin Gaza a masallcin darulkutni da ke gabacin yankin, tare da halartar wasu daga cikin jami’an gwamnatin yankin Zirin Gaza.
750333


captcha