Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Bosnia ya yi ishara da cewa, babban abin da zai karfafa hadin kan musulmi tare da zama tsiya daya madaurinki daya shi ne yin aiki da koyarwar addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na taron hadin kan al'ummar musulmi da ake gudanarwa abirnin Tehran babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Bosnia ya yi ishara da cewa, babban abin da zai karfafa hadin kan musulmi tare da zama tsiya daya madaurinki daya shi ne yin aiki da koyarwar addinin musulunci baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa abin da musulmi suke da banbanci a kansa lamari na siyasa, amma asalin addini guda daya ne kuma banbancin dalilai kan furu'a ba shi ne abin da zai raba haduwar musulmi kan addinin guda daya ba, inda ya buga misali da aikin haji da dukkanin musulmi duk kuwa da banbancin mazhabobinsu suke taruwa wuri guda.
Babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Bosnia ya yi ishara da cewa, babban abin da zai karfafa hadin kan musulmi tare da zama tsiya daya madaurinki daya shi ne yin aiki da koyarwar addinin musulunci a cikin rayuwar zamantakewar musulmi
750634