IQNA

Za A Fara Gudanar Da Wani Baje Kolin Kayan fasahar Musulunci Na Zamani A Amurka

18:46 - February 21, 2011
Lambar Labari: 2084264
Bangaren kasa da kasa, Ana shirin fara gudanar da wani babban baje kolin kayan fasahar zamani na addinin muslunci a jahar Penselvania da ke kasar Amurka, da nufin kara fito da matsayin addinin muslunci ga al'aummar kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic Art Magazine an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani babban baje kolin kayan fasahar zamani na addinin muslunci a jahar Penselvania da ke kasar Amurka, da nufin kara fito da matsayin addinin muslunci ga al'aummar kasar da mafi yawansu suke da karancin fahimta kan asalin addinin muslunci balanta koyarwarsa.

Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin wannan baje koli za a nuna wasu daga abubuwa da suka shafi fasahar addinin muslunci a zamanance, tare da fitar da abubuwan da addinin muslunci ya ginu a kansu kuma yake kiran 'yan adam zuwa gare su, maimako yadda suke da karkatattar fahimta kansa.

Ana shirin fara gudanar da wani babban baje kolin kayan fasahar zamani na addinin muslunci a jahar Penselvania da ke kasar Amurka, da nufin kara fito da matsayin addinin muslunci ga al'aummar kasar Amurka baki daya.

750962






captcha