Bangaren al'adu da fasaha, Za a gudanar da zaman taron maulidin manzon Allah (SAW) da Imam Ja'afar Sadiq (AS) a birnin Laknu na kasar India, wanda cibiyar bunkasa harkokin al'adu da zamantakewar jama'a ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa akasar India cewa, za a gudanar da zaman taron maulidin manzon Allah (SAW) da Imam Ja'afar Sadiq (AS) a birnin Laknu na kasar India, wanda cibiyar bunkasa harkokin al'adu da zamantakewar jama'a ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a daren yau.
Taron zai samu halartar mabiya addinin musulunci da ke zaune a birnin da kuma wakilan kungiyoyin bincike da suka hada da na mabiya sunna da kuma mabiya amzhabar yalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa.
Manzon Allah (SAW) yana dauke da sakon haske ne ga dukkanin 'yan adam daga Allah madaukakin sarki, domin shiryar da su zuwa ga abin da mahaliccinsu ya halicce su don shi, a kan haka ne zaman taron ya mayar da hankali kan ayar da ke tabbatar da cewa manzon yana kan kyawawan dabi'u.
750749