Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridarArab news an habarta cewa, ofishin jakadancin kasar Faransa a kasar saudiyya ya shirya gudanar da wani taro kan fasahohin muslunci a tarihi, tare da baje koli na kayyakin fasaha da ke nuni da daddun ala'du da suke a cikin koyarawar addinin musulunci tun zamunan da suka shude.
Taron yana yin dubi ne kan matsayin addinin musulunci a matasayin daya daga cikin manyan addinai na duniya, wanda ya taka gagarumar rawa a dukkanin fannonin na rayuwar dan adam, tare da koyar da shi hanyoyi na zamantakewa a tsakanin dukkanin al'ummomi.
Ofishin jakadancin kasar Faransa a kasar saudiyya ya shirya gudanar da wani taro kan fasahohin muslunci a tarihi, tare da baje koli na kayyakin fasaha da ke nuni da daddun ala'du da suke a cikin koyarawar addinin musulunci ga bil adama.
751762