IQNA

Imam Musa Sadr Ya Raya mazhabar Iyalan Gidan Manzo A Kasar Lebanon

19:23 - February 23, 2011
Lambar Labari: 2085546
Bangaren kasa da kasa, Imam Musa Sadr ya raya tafarkin iyalan gidan manzo a Lebanon, ta hanyar yin amfani da salo da hanyoyi na hankali da ilimi da Allah madaukakin sarki yah ore masa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishinsa ya habarta cewa, ya gudanar da wata zantawa da daya daga cikin malamai kuma shugaban bangaren bunkasa harkokin al'adu na Iran a Lebanon Sayyid Muhammad Hussain inda ya bayyana cewa, Imam Musa Sadr ya raya tafarkin iyalan gidan manzo a Lebanon, ta hanyar yin amfani da salo da hanyoyi na hankali da ilimi da Allah madaukakin sarki ya hore masa a rayuwarsa mai albarka.
A wani bangare kuma daya daga cikin masu adawa da gwamnatin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya da ke zaune a birnin London na kasar Birtaniya ya sheda cewa, Imam Musa Sadr da Gaddafi ya kama shi tun sama da shekaru talatin da suka gabata yana tsare a wani gidan kaso da ke kudanci Libya.
Ya ce mahukuntan kasar Libya sun sha yin karya dangane da makomar Imam Musa Sadr bayan da suka kame shi a lokacin da yake gudanar da wata ziyara a kasar, bayan da Gaddafi ya gayyace shi, inda suke cewa ya bar kasar, amma dukkanin dalilai sun tabbata da cewa yana nan tsare.
750562



captcha