IQNA

Allah Ya Yi Babban Malamin Addini Ayatollah Sayyid Muhammad Ali Hakim Rasuwa

10:22 - February 27, 2011
Lambar Labari: 2086955
Bangaren kasa da kasa, A jiya ne Allah ya yi wa babban malamin addinin muslunci Ayatollah Ozma Sayyid Muhammad Ali Hakim rasuwa a birnin Najaf mai alfarma da ke kasar Iraki.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a labarin da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran Brana an bayyana cewa, a jiya ne Allah ya yi wa babban malamin addinin muslunci Ayatollah Ozma Sayyid Muhammad Ali Hakim rasuwa a birnin Najaf mai alfarma da ke kasar Iraki, kuma an fara gudanar da janazarsa daga birnin karbala mai alfarma, inda za a rufe gawarsa a birnin Najaf.

Babban malamin dai mahaifi ne ga daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Muhammad sa'id Hakim, malamin ya rasu ne yana da shekaru 100 da haihuwa aduniya, an haife shi ne a garin Najaf a cikin shekara ta 1329 kamariya.

Ya kasance daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci da mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah ke komawa zuwa gare su, ya rubuta manyan littafai a fagage da daman a ilimin addinin Musulunci, musamman ma a bangaren fikihu da usul.

Ya kasance limami a birnin Najaf mai alfarma, kamar yadda ya zama babban abin buga misali a bangaren tsoron Allah da nuna kyakwawan dabi'u, da kuma kaskantar da kai ga muminai, haka nan kuma ya samar da manyan malaman addini daga almajiransa.

753846






captcha