IQNA

An Rufe Wani Shafin Yanar Gizo Da Ke Cin Zarafin Musulunci A Kasar Pakistan

10:36 - March 03, 2011
Lambar Labari: 2089500
Bangaren kasa da kasa, An rufe wani shafin yanar gizo da ke cin zarafin addinin musulunci a kasar Pakistan, wanda gwamnatin kasar ta daukin nauyin yin hakan domin takawa masu kiyayya da musulunci birki kan abubuwan tsokana da suke yi kan musulunci.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin yanar gizo na Times od India cewa, an rufe wani shafin yanar gizo da ke cin zarafin addinin musulunci a kasar Pakistan, wanda gwamnatin kasar ta daukin nauyin yin hakan domin takawa masu kiyayya da musulunci birki kan abubuwan tsokana da suke yi kan musulunci da musulmi ta hanayar yin batunci ga ababe masu tsarki.
Bayanin ya ci gaba da cewa mataimakin ministan ma’aikatar shari’a na kasar ta Pakistan ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa cibiyar da ke kula da ayyukan sadarwa ta kasar, ta fara gudanar da aikin rufe shafukan da suke yin batunci ga addinin muslunci, ta hanyar tozartya kur’ani mai tsarki, ko manzon Allah (SAW) wanda hakan babbar tsokana ce mabiya addinin musulunci.
Rufe shafin yanar gizo da ke cin zarafin addinin musulunci a kasar Pakistan, wanda gwamnatin kasar ta daukin nauyin yin hakan domin takawa masu kiyayya da musulunci birki kan abubuwan tsokana da suke yi kan musulunci, babban mataki na kare ababe masu tsarki a addinin musulunci.
756618

captcha