Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani zaman taro da ke yin dubi kan tarihin rayuwar ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a birnin Islam-abad fadar mulkin kasar pakistan a yau.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na The News an habarta cewa, an fara gudanar da wani zaman taro da ke yin dubi kan tarihin rayuwar ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a birnin Islam-abad fadar mulkin kasar pakistan a yau Talata.
Wannan zaman taro dai yana yin dubi ne kan kan irin gagarumar gudunmawar da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan gidansa ya bayar wajen raya ruhin ‘yan adamtaka a cikin rayuwarsa, da bayyana hakikanin koyarwar addinin muslunci a cikin dyukkanin ayyukansa kamar yadda Allah ya umurce shi.
An fara gudanar da wani zaman taro da ke yin dubi kan tarihin rayuwar ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a birnin Islam-abad fadar mulkin kasar pakistan a yau.
759142