Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Haveeru an bayyana cewa, Bankin musulunci na farko ya fara gudanar da ayyukansa a kasar Maldev, da nufin gudanar da ayyuka ta fuskancin harkokin kudi da kasuwanci bisa ka’idoji da koyarwar addinin musulunci, wanda ya samu karbuwa daga mafi yawan al’ummar kasar wadda akasarin mazaunanta mabiya addnin muslunci ne.
Rahoton ya ce an bude bankin ne tare da halartar shugaban kasar Muhammad Nashid, a nasa bangaren kuwa babban daraktan bankin Haris harun ya bayyana cewa, an bude bankin domin gudanar da harkokin banki bisa kaida da shari’a ta addnin musulunci, sakamakon kiraye-kirayen da al’ummar kasar suka yi da ke neman a samar da irin wannan banki.
Bankin musulunci na farko ya fara gudanar da ayyukansa a kasar Maldev, da nufin gudanar da ayyuka ta fuskancin harkokin kudi da kasuwanci bisa ka’idoji da koyarwar addinin musulunci, wanda ya samu karbuwa daga mafi yawan al’ummar kasar.
760425