IQNA

18:31 - March 11, 2011
Lambar Labari: 2093822

An Gudanar Da Zaman taron Taron Daliban Jami’a Musulmi Na Kasar Serraliyon

Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar da zaman taro na wayar da kan daliban jami’a musulmi da ke kasar saliyo, domin tunatar da su muhimman abubuwan da suka rataya kansu na aiki da koyar addinin musulunci kamar yadda manzon tsira ya zo da shi, ta yadda hakan zai yi tasiri wajen baayyana wa sauran dalibai hakikanin musulunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya samu daga bangaren yada labaransa a nahiyar Afirka an bayyana cewa, an gudanar da zaman taro na wayar da kan daliban jami’a musulmi da ke kasar saliyo, domin tunatar da su muhimman abubuwan da suka rataya kansu na aiki da koyar addinin musulunci kamar yadda manzon tsira ya zo da shi, ta yadda hakan zai yi tasiri wajen baayyana wa sauran dalibai hakikanin musulunci da kur’ani da kuma koyarwarsu.
Wannan zaman taron dai an gudanar da shi ne tare da hadin gwiwa da babbar kungiyar daliban musulmin kasar Saliyo da kuma cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta kasar Iran, wanda babban ofishinta da ke kasar ta Saliyo ya dauki nauyin gudanarwa a cikin wannan mako.
an gudanar da zaman taro na wayar da kan daliban jami’a musulmi da ke kasar saliyo, domin tunatar da su muhimman abubuwan da suka rataya kansu na aiki da koyar addinin musulunci kamar yadda manzon tsira ya zo da shi, ta yadda hakan zai yi tasiri wajen baayyana wa sauran dalibai hakikanin musulunci.
760914

captcha