IQNA

17:56 - March 13, 2011
Lambar Labari: 2095094

Kasashen Yammacin Turai Ba Za Su Iya Tsayar Gaba Kan Addinin Musulunci Ba

Bangaren siyasa da zamantakewa, wanda ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Beirut Sayyid Ali Fadlollah ya bayyana cewa lokaci ya yi da kasashen yammacin za su fahinci cewa yanzu ba lokaci ne na izgili da nuna kyama ga sauran addinai ba, lokaci ne ya wayewa da sanin manufa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon cewa, wanda ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Beirut Sayyid Ali Fadlollah ya bayyana cewa lokaci ya yi da kasashen yammacin za su fahinci cewa yanzu ba lokaci ne na izgili da nuna kyama ga sauran addinai ba, lokaci ne ya wayewa da sanin manufa a cikin rayuwa.

Malamin ya ci gaba da yin ishara da cewa, a koda yaushe addnin Musulunci ya kasance cikin kariya ne daga hare-haren da yake fuskanta daga makiya a tsawon tarihi, haka nan kuma irin gabar da makiya addinin muslunci suka dauka a tarihi ita ce ake ganin tana maimaita kanta a tsakanin al'ummomin kasashen turai tare da karfafar gwiwa daga mahukuntansu.

wanda ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Beirut Sayyid Ali Fadlollah ya bayyana cewa lokaci ya yi da kasashen yammacin za su fahinci cewa yanzu ba lokaci ne na izgili da nuna kyama ga sauran addinai ba, lokaci ne ya wayewa da sanin manufa.

762138
captcha