IQNA

16:08 - March 16, 2011
Lambar Labari: 2097090

An Fara Gudanar Da Wani Zaman Taro Na Malaman Addinin Musulunci A Burnei

Bangaren kasa da kasa, malaman makarantu da ke koyar da ilmomin addinin musulunci a makarantun kasar Burnei sun gudanar da wani zaman taro, wanda shi ne irinsa na farko da suka taba gudanarwa, domin yin nazari yadda darussan musulunci ke yin tasiri tsakanin dalibai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na RTBN an bayyana cewa, malaman makarantu da ke koyar da ilmomin addinin musulunci a makarantun kasar Burnei sun gudanar da wani zaman taro, wanda shi ne irinsa na farko da suka taba gudanarwa, domin yin nazari yadda darussan musulunci ke yin tasiri tsakanin dalibai a dukkanin makarantun kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka dukkanin malaman sun gabatar da bayanan da suke dauke da su ga zaman taron nasu, inda akasari suka yi ishara da gagarumin tasirin da darussan addinin musulunci suke da shi a tsakanin dalibai, kasantuwar kasar ta musulmi kuma masu matukar himma.
Malaman makarantu da ke koyar da ilmomin addinin musulunci a makarantun kasar Burnei sun gudanar da wani zaman taro, wanda shi ne irinsa na farko da suka taba gudanarwa, domin yin nazari yadda darussan musulunci ke yin tasiri tsakanin dalibai da kuma samar da hanyoyin karfafa su.
764138

captcha