IQNA

23:06 - March 16, 2011
Lambar Labari: 2097163

An TarJama Juzu’in Kur’ani Na Talatin A Cikin Harsunan Sawahili Da Fulatanci

Bangaren kasa da kasa, an tarjama juzu’i na talatin na kur’ani mai tsarki a cikin harsunan sawahili da kuma fulatanci wanda wanda cibiyar bunkasa harkokin al’adu da ilimi ta kasashen musulmi ta dauki nauyinsa, an buga kwafin ne a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, an tarjama juzu’i na talatin na kur’ani mai tsarki a cikin harsunan sawahili da kuma fulatanci wanda wanda cibiyar bunkasa harkokin al’adu da ilimi ta kasashen musulmi ta dauki nauyinsa, an buga kwafin ne a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan a cikin wannan mako.
A bangare guda kuma bayanin ya yi nuni da cewa an gudanar da wannan zaman taro ne da nufin kara karfafa mabiya addinin musulunci kan sanin addininsu da kuma tarihin manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, wanda hakan ne zai ba su damar yin aiki da koyarwa a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar zamantakewa.
An gudanar da wani zaman taro na mabiya addinin musulunci a yankin Rajuri na yankin keshmir, wanda ya samu halartar daruruwan malaman addini da kuma mutanen yankin wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne.
764077


captcha