IQNA

17:45 - March 26, 2011
Lambar Labari: 2098102

Zaman taro Na Kasa Kan Shahidan Bayar Da Agaji a Cikin Shekara Ta 1390

Bangaren zamantakewa, babban mai bayar da shawara ga cibiyar bayar da agaji ta Helal Ahmar a jamhuriyar musulunci ya bayyan a cewa, a cikin watan gobe za su gudanar da zaman taro na tunawa da shahidan bayar da agaji.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, babban mai bayar da shawara ga cibiyar bayar da agaji ta Helal Ahmar a jamhuriyar musulunci ya bayyan a cewa, a cikin watan gobe za su gudanar da zaman taro na tunawa da shahidan bayar da agaji a fadin kasa.
A bangare guda kuma wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine info an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta fitar da wani bayani da a cikinsa take bayyana halin da al’ummar yankin Gaza suke ciki na kunci, da hakan ya hada da rashin wutar lantarki da kuma karancin tsaftataccen ruwan sha a yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akari da yadda haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya ta saka al’ummar yanki cikin wani yanayi na kurkuku, yanayin rayuwarsu sai kara zama cikin muni yake yi, domin kuwa yanzu haka akwai wasu asibitoci da suek fama da karancin magunguna, kamar yadda wutar lantarki a yankin har yanzu ba ta tabbata ba.
757996

captcha