Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarain da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran an bayyana cewa, a yau ne za a gudanar da zaman taro na sabuwar shekarar shamsiyya a birnin Tehran, tare da halartar shugabannin kasashe masu magana da harshen farisanci, kamar yadda UNESCO ta tabbatar da hakan a hukumance.
A lokacin da yake tarbar wasu daga cikin bakin da za su halarci zaman taron a yammacin jiya a nanan birnin Tehran, shugaba Ahmadinejad ya bayyana cewa bababr manufar gudanar da wannan zaman taro dai ita ce kara karfafa danganta tsakanin kasashen yankin banki daya, wadanda abubuwa da dama suka hada su.
Daga ciki kuwa har da addini da kuma tsohuwar dangantaka ta al'adu, wanda a cewarsa kasashen yankin za su iya aiwatar da abubuwa da daman a hadin gwiwa da za su amfanar da al'ummominsu, ba tare da wani ya yi musu katsalandan ba.
Daga cikin wadanda za su halarci taron har shugabannin kasashen Afghanistan, Tajikistan, Armenia, Turemenista da kuma Iraki, gami da yarima mai jiran gado na kasar Qatar, da kuma ministoci daga kasashen Oman, India, Kuwait da dai sauransu.
763332