Bangaren kasa da kasa, wani fitaccen dan siyasa a kasar birtaniya kuma mamba ajamiyar BNP da ke neman kujerar dan majalisar dokokin kasar a karkashin inuwar wannan jam’iyya daga Wolse, yaana neman amincewar ‘yan majalisar da takararsa amma tahanyar cin zarafin musulmi da keta alfamar kur’ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Times of Pakistan cewa, wani fitaccen dan siyasa a kasar birtaniya kuma mamba ajamiyar BNP da ke neman kujerar dan majalisar dokokin kasar a karkashin inuwar wannan jam’iyya daga Wolse, yana neman amincewar ‘yan majalisar da takararsa amma tahanyar cin zarafin musulmi da keta alfamar kur’ani mai tsarki.
A cikin wani bayani da ta fitar kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allawadai da keta alfarmar alkur’ani mai tsarki da wani mai kiran kansa malamin addinin kirista ya yi a kasar Amurka, tare da bayyana hakan da cewa wani mataki ne da ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinai, bababn sakataren kungiyar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin jakadojin kasashen musulmi.
A bangare guda kuma bayanin ya yi nuni da cewa an gudanar da wannan zaman taro ne da nufin kara karfafa mabiya addinin musulunci kan sanin addininsu da kuma tarihin manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, wanda hakan ne zai ba su damar yin aiki da koyarwa a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar zamantakewa. 772416