Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic Studies Network an bayyana cewa, a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya, kuma wannan shi ne karon farko da za agudanar da irinsa.
A yayin gudanar da zama masana da malaman jami’oi za su halarta kuma za su gabatar da laccoci ga mahalrta taron, daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai nazari kan matsayin sharia a cikin addinin muslunci, da kuma yadda wannan addini mai tsarki yake kallon rayuwar zamantakewa ta jama’a.
Rahoton ya tabbatar da cewa a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani zama na karawa juna sani kan nazarin addinin musulunci, wanda za a gudanar a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Lise da ke kasar Birtaniya a karon farko.
773755