IQNA

Bangaren siyasa da zamantakewa: za a gudanar da jerin tarurrukan shekara shekara na yada addini a kasar Indiya kuma daga ranar takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne a huseiniyar hadarat Kasim (AS) da ke garin Jalalpur a lardin Utarparadesh za a gudanar.Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; za a gudanar da jerin tarurrukan shekara shekara na yada addini a kasar Indiya kuma daga ranar takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne a huseiniyar hadarat Kasim (AS) da ke garin Jalalpur a lardin Utarparadesh za a gudanar. A kowace shekara ana gudanr da irin wannan taro da ke kula da harkokin da suka shafi addini da kuma hanyoyin day a dace a bi wajan yadawa da kuma binkasa addinin musulunci a kasar ta indiya inda mashahuran malamai ke tattaunawa da gabatar da jawabai.


775365