Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birinin Beirut a kasar Lebanon an bayyana cewa, manyan malaman addinin muslunci a kasar Lebanon sun yi kakkausar suka da kuma yin Allawadai da cin zarafin da mahukuntan kasashen Bahrain da Saudiyya suke yi kan al'ummar Bahrain, ta hanyar murkushe zanga-zangarsu ta lumana da karfin tuwo, da kuma afkawa kan masallatansu da wuraren ibadarsu da nufin wanzuwar sarautar kasashen biyu ta kama karya.
Bayanin ya ci gaba da cewa akwai wasu daga cikin masu kokarin nuna abin da ke faruwa a kasar Bahrain a matasayin wani lamari na mazhaba ko bangaranci tsakanin al'umma da kuam mahkunta, wanda hakan ya yi hannun riga da abin da ya ke gaskiya a kasar ta Bahrain, inda mutane suke bukatar da a gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin siyasar kasar, maimakon tafiya kan tafarkin yanzu.
Manyan malaman addinin muslunci a kasar Lebanon sun yi kakkausar suka da kuma yin Allawadai da cin zarafin da mahukuntan kasashen Bahrain da Saudiyya suke yi kan al'ummar Bahrain, ta hanyar murkushe zanga-zangarsu ta lumana da karfin tuwo, da kuma afkawa kan masallatansu da wuraren ibadarsu da nufin wanzuwar sarautar kasashen biyu.
776340