IQNA

Makarancin Kur’ani Daga Iran Ya Samu Karbuwa A Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kuwait

13:56 - April 20, 2011
Lambar Labari: 2109154
Bangaren kasa da kasa, makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke karawa da juna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke karawa da juna domin nuna irin baiwar da Allah madaukakin sarki ya yi musu.
Makarnaci ya samu kyakkyawar karbuwa daga su kansu makaranta da suke halartar wannan gasa daga kasashen duniya daban-daban musamman na musulmi da na larabawa, kamar yadda kwamitin shirya gasar ya nuna matukar gamsuwa da yadda yake yin amfani da salo na musamman wajen karanta littafin Allah mai tsarki, bayan kammala gasar dai za abayar da kyutuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.
makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke gogawa da junasu.
776862


captcha