IQNA

An fara Rijistar Sunayen Masu Sha’awar Shiga Gasar Karatun Kur’ani A Masar

14:46 - April 20, 2011
Lambar Labari: 2109214
Bangaren kasa da kasa, an fara rijistar sunayen masu sha’awar shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Masar, wadda za a fara gudanarwa amataki na kasa, daga bisani kuma za a gudanmar da abbar gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya baki daya a kasar, tare da halartar mahardata da makaranta daga sassa na kasashen duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalti daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd an bayyana cewa, an fara rijistar sunayen masu sha’awar shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Masar, wadda za a fara gudanarwa amataki na kasa, daga bisani kuma za a gudanmar da abbar gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya baki daya a kasar, tare da halartar mahardata da makaranta daga sassa na kasashen duniya musamman na larabawa da na musulmi.
A bangare guda kuma an fara gudanar da taron baje koli na kayan fasahar masana a musulunci a kasar Birtaniyam, wanda babbar cibiyar kula da kayan tarihin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tun daga makon da ya gabata a babban dakin tarukanta da ke birnin London fadar mulkin kasar.
Taron yana samun halartar masana kan harkokin al’adu da tarihi daga jami’ar birnin London da kuma wasu cibiyoyi na mabiya addinin muslunci da ke cikin sassan kasar, haka nan kuma ana nuna wasu daga cikin abubuwan da aka samar na fasahar musulunci a kasar weadanda suke nuna kokarin masana musulmi masu fasaha da suke gudanar da ayyuka a wannan bagire.
776922
captcha