Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizona SPA an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya Ikmaluddin Auglo ya bayyana cewa kungiyar a shirye take ta shirya wani zaman taro kan yaki da ta'addanci a tare da halartar wakilan kasashen duniya da suka hada da na musulmi da ma wadanda ban a musulmi ba, domin sanin matsayin addinin Musulunci kan ayyukan ta'addanci.
Ya ci gaba da cewa addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai, kuma danganta ayyukan ta'addanci da addinin muslunci babban zalunci ne da keta huruminsa, kuma yin hakan ya tabbar da jahiltar muslunci da koyarwa a tsakanin 'yan adam.
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya Ikmaluddin Auglo ya bayyana cewa kungiyar a shirye take ta shirya wani zaman taro kan yaki da ta'addanci a tare da halartar wakilan kasashen duniya da suka hada da na musulmi da ma wadanda ban a musulmi ba, domin sanin matsayin addinin Musulunci kan dukkanin harkokin rayuwar jama'a ta zamantakewa.
777656