Bangaren kasa da kasa, mabiya addinai daban-daban na kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu mabiya addinin kirista suka yi a kasar da sunan yunkurin bayyana ra'ayinsu, wanda ake ganin hakan wani aiki ne na tsokana ga al'ummar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na islam on line an bayyana cewa, mabiya addinai daban-daban na kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu mabiya addinin kirista suka yi a kasar da sunan yunkurin bayyana ra'ayinsu, wanda ake ganin hakan wani aiki ne na tsokana ga al'ummar musulmi na kasar Amurka da sauran kasashen duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai wasu daga cikin mabiya addinin kirista da suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan lamari, wanda mabiya addinan suke ganin cewa idan ba a dauki matakan kawo karshen hakan ba, za a iya fadawa cikin wani mawuyacin hali tsakanin dukkanin al'immomin duniya..
mabiya addinai daban-daban na kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu mabiya addinin kirista suka yi a kasar da sunan yunkurin bayyana ra'ayinsu, wanda ake ganin hakan wani aiki ne na tsokana ga al'ummar musulmi.
778667