Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, Mgr Podvin babban mai magana da yawun kwamitin anyan malaman addinin kirista a kasar Faransa ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar take tafiyar da siyasarta kan mabiya addinin muslunci kuma marassa rinjaye a kasar,inda ake nuna musu banbanci na zahiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na le-coran an bayyana cewa, an saka tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin shafin yanar gizo a cikin harshen farasanci, tare da karatun kur’ani mai tsarki daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, da nufin kara fadada ayyukan kur’ani a shafukan yanar gizo da ake ziyarta koina.
Bayan wannan tarjamar kur’ani mai tsarki a acikin harshen faranci dake cikin wannan shafi na yanar gizo, za a iya sanin wasu abubuwan da suka shafi kur’ani, kamar sanin adadin ayoyin da ke cikin sura, ko kuma dalilan safkar ayoyi da kuma tafsirin ma’nar wasu kalmomin kur’ani, da suke bukar bayani ta yadda mai karatu ba zai sha wahala wajen gane ma’narsu ba ga masu nazari.
782265