IQNA

13:20 - April 30, 2011
Lambar Labari: 2113994

Hukuncin Kisa Kan Masu Zanga-Zanga Ya Kara Fito Da Zaluncin Mahukuntan Bahrain

Bangaren kasa da kasa, hukuncin kisa da wata kotun soji da mahukuntan kasar Bahrain ta yanke kan masu gudanar da zanga-zangar lumana a kasar, hakan ya kara fito da matsayin mahukuntan kasar na zalunci da danniya kan al'ummar kasar marassa kariya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo an bayyana cewa, Kungiyar tarayyar turai ta yi kakkausar suka kan hukuncin kisa da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan wasu matasa da suka shiga zanga-zangar neman sauyi a kasar.

Kakakin kungiyar tarayyar turai Jerzy Buzek, ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa a kasar.

A jiya ne wata kotun soji da mahukuntan Bahrain suka kafa cikin makwannin suka, ta yanke hukuncin kisa kan wasu matasa hudu, bisa zargin cewa suna da hannu wajen mutuwar 'yan sanda biyu a lokacin gudanar da zanga-zanga a birnin Manama.

Al'ummomin duniya da dama da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, suna ci gaba da yin Alawadai da mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya, sakamakon yin amfani da karfin soji da suka yi wajen yin kisan gilla a kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa ta hanyar lumamana a cikin kasar ta Bahrain.


782975

captcha