IQNA

20:27 - May 01, 2011
Lambar Labari: 2115417

An Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Bahrain A Saudiyya

Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman sarakunan kasar gami da na kasar Saudiyya.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid an bayyana cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman sarakunan kasar gami da na kasar Saudiyya, tun daga lokacin da suka fara gudanar da gangamin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar.
A wani labarin kuma makamanicn wannan kungiyar tarayyar turai ta yi kakkausar suka kan hukuncin kisa da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan wasu matasa da suka shiga zanga-zangar neman sauyi a kasar.
Kakakin kungiyar tarayyar turai Jerzy Buzek, ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa a kasar.
A jiya ne wata kotun soji da mahukuntan Bahrain suka kafa cikin makwannin suka, ta yanke hukuncin kisa kan wasu matasa hudu, bisa zargin cewa suna da hannu wajen mutuwar 'yan sanda biyu a lokacin gudanar da zanga-zanga a birnin Manama.
Al'ummomin duniya da dama da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, suna ci gaba da yin Alawadai da mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya, sakamakon yin amfani da karfin soji da suka yi wajen yin kisan gilla a kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa ta hanyar lumamana a cikin kasar.
783396



captcha