Bangaren kasa da kasa, an nuna wasu daga cikin littafan da aka rubuta kan ayyukan bincike da suka danganci ilmomin kur’ani a kasuwar baje kolin duniya da ake gudanarwa a birnin Tehhran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran, da ke samun halartar masana da kuma cibiyoyin ilimi na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo, an nuna wasu daga cikin littafan da aka rubuta kan ayyukan bincike da suka danganci ilmomin kur’ani a kasuwar baje kolin duniya da ake gudanarwa a birnin Tehhran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran, da ke samun halartar masana da kuma cibiyoyin ilimi na duniya da kuma na cikin gida.
Wwani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na le-coran an bayyana cewa, an saka tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin shafin yanar gizo a cikin harshen farasanci, tare da karatun kur’ani mai tsarki daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, da nufin kara fadada ayyukan kur’ani a shafukan yanar gizo da ake ziyarta koina cikin duniya.
Bugu da kari kan tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin harshen faranci dake cikin wannan shafi na yanar gizo, za a iya sanin wasu abubuwan da suka shafi kur’ani, kamar sanin adadin ayoyin da ke cikin sura, ko kuma dalilan safkar ayoyi da kuma tafsirin ma’nar wasu kalmomin kur’ani, da suke bukar bayani ta yadda mai karatu ba zai sha wahala wajen gane ma’narsu ba.
788353