Bangaren siyasa da zamantakewa: a jiya ne sha tara ga watan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'uin hijira shamsiya musulmin kasar Tailand suka gudanar da wani gagaramin taron nuna adawarsu da matakin hana yan makaranta mata sanya hijabi a makarantun Wat Nong Chok kuma sun gudanar da wannan taro ne a gaban makarantar domin nuna bacin ransu a fili da wannan mataki na nuna wariya da banbanci.