IQNA

Za A Bude Wata Sabuwar Jami'ar Addinin Musulunci A kasar Malazia

15:58 - May 12, 2011
Lambar Labari: 2121040
Bangaren kasa da kasa, za a bude wata sabuwar jami'ar muslunci a jahar Penang a kasar Malazia, da nufin kara bunkasa harkokin addinin Musulunci da iliminsa a kasar, wanda hakan ya samu karbuwa daga mutanen yankin.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama an bayyana cewa, za a bude wata sabuwar jami'ar muslunci a jahar Penang a kasar Malazia, da nufin kara bunkasa harkokin addinin Musulunci da iliminsa a kasar, wanda hakan ya samu karbuwa daga mutanen yankin baki daya.

Bayanin ya ci gab ada cewa wannan jami'ar za ta taka gagarumar rawa a fuskacin ilimi da kuma yada al'adun addinin musluncici, bisa la'akari da cewa kasar Malazia kasa ce da ta shahara ta fskacin yawan musulmi, da kuma bayar da gudunmawa wajen yada ilimin wannan addini a cikin kasar da ma kasashen yankin.

Za a bude wata sabuwar jami'ar muslunci a jahar Penang a kasar Malazia, da nufin kara bunkasa harkokin addinin Musulunci da iliminsa a kasar, wanda hakan ya samu karbuwa daga mutanen yankin Asia.

789600




captcha