Bangaren siyasa da zamantakewa;Ruza Atan Bayuva shugaban kasar Karkazistan a ranar talatar da ta gabata ranar uku ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya gana da Cubak Haji Jalil Uf babban mai fitar da fatawa a wannan kasa ta Karkizistan inda suka tattaunawa kan lamuran da suka shafi kasar.