IQNA

Cibiyar Ayyukan Addini Ta ‘Yan Shi’ar Bahrain Ta Bukaci Da A Gyaran Masallatan Da Aka Rusa

16:49 - May 28, 2011
Lambar Labari: 2129706
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da ayyukan addinin muslunci ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Bahrain ta aike da wata wasika zuwa ga sarkin kasar, da ke nemansa da gyara dukkanin masallatan da rusa da sauran gine-ginen cibiyoyinsu na addini ba tare da ba ta lokaci ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, cibiyar kula da ayyukan addinin muslunci ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Bahrain ta aike da wata wasika zuwa ga sarkin kasar, da ke nemansa da gyara dukkanin masallatan da rusa da sauran gine-ginen cibiyoyinsu na addini ba tare da ba ta lokaci ba tare da dora alhakin dukkanin abin da ya faru a kansa.
Tun bayan da al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da zanga-zangar neman sauyina siyasa a cikin harkokin mulkin kasar, sarkin ya aike da goron gayyata zuwa ga gwamnatin wahabiyawan Saudiyya yana neman dauki, inda inda Amurka ta baiwa Sdaudiyya damar aikeawa da dakarunta domin murkushe duk wani da ya gudanar da zanga-zangar lumana a kasar, tare da yi musu kisan gilla.
Babbar cibiyar kula da ayyukan addinin muslunci ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Bahrain ta aike da wata wasika zuwa ga sarkin kasar, da ke nemansa da gyara dukkanin masallatan da rusa da sauran gine-ginen cibiyoyinsu na addini ba tare da ba ta lokaci ba, kuma rashin yin hakan zai kara tabbatar da laifinsa bisa dokoki na kasa da kasa. 799094
captcha