IQNA

Majalisar Birnin Sarvece Na Switzerland Ta Hana Mai Gaba Da Musulunci Yin Jawabi

13:48 - May 29, 2011
Lambar Labari: 2130204
Bangaren kasa da kasa, majalisar birnin Service na kasar Switzerland ta dauki wani mataki nah an adan majalisar kasar Holland din nan mai matukar adawa da addinin Musulunci gabatar da wani jawabi a birnin, bayan da wasu masu irin ra'ayinsa suka gayyace shi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, majalisar birnin Service na kasar Switzerland ta dauki wani mataki nah an adan majalisar kasar Holland din nan mai matukar adawa da addinin Musulunci gabatar da wani jawabi a birnin, bayan da wasu masu irin ra'ayinsa suka gayyace shi domin gabatarwa.

A wani labari da ya nakalto daga shafin yanar giz na atlainfo an bayyana cewa, babban daraktan cibiyar addnin muslunci da kuma babban masallacin birnin Lion na kasar Faransa Kamil Kabtan ya bayyana cewa, wannan masallacin da kowa da kowa ne, ba kamar yadda jami’an ma’aiktar tsaron kasar Amurka suka fada ba kan cewa wuri ne na taruwar ‘yan ta’adda da suke yin barazana ga nahiyar turai.
Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin mabiya addinin muslunci suna hakki su zo su gudanar da lamurran ibada acikin masallaci daga ko’ina cikin duniya, kuma abin da jami’an na ma’aikatar tsaron kasar Amurka suka fada babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin kuwa dukkanin mabiya addinin msulunci sun yi imani da zaman lafiya tsakaninsu da sauran mabiya addinai.

799568


captcha